Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO ta yabawa yadda kasar Sin ta tunkari cutar COVID-19 da aka samu a tsakanin wasu rukunonin al'umma
2020-06-20 16:27:03        cri
Wani babban jami'in hukumar lafiya ta duniya WHO, ya ce kasar Sin ta yi kokari sosai, wajen dakile yaduwar cutar COVID-19 da aka samu tsakanin wasu rukunonin jama'a.

Babban Daraktan shirin lafiya na gaggawa na hukumar, Dr Michael Ryan ne ya bayyana haka jiya a Geneva, yayin wani taron manema labarai.

Da yake bada kyawawan misalai da Jamus da Japan da Koriya ta kudu, Dr. Ryan ya bayyana cewa, ya san takwarorinsu a Beijing sun shirya gaggarumin aikin tunkarar cutar, a yunkurinsu na hana yanayin tsananta, yana mai bayyana muhimmancin gaggawar gano cutar da gudanar da bincike da kuma dakile barkewarta a tsakanin rukunonin jama'a.

Baya ga haka, ya ce babu wani abu takamaimai dake bayyana cewa an samu sabon zagayen barkewar cutar, yana mai cewa, samun cutar a tsakanin wani rukunin jama'a, baya nufin wani sabon zagaye na barkewarta. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China