Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO ta bada rahoton adadi mafi yawa na masu kamuwa da COVID-19 a rana guda
2020-07-05 16:05:46        cri
Hukumar lafiya ta duniya WHO a ranar Asabar ta fitar da rahoton sabbin alkaluma da ya kai 212,326 na wadanda suka kamu da cutar COVID-19 cikin sa'o'i 24 da suka gaba, wannan shi ne adadi mafi yawa na sabbin masu kamuwa da cutar COVID-19 a rana guda tun bayan barkewarta.

Adadi mafi yawa na alkaluman an same su ne a nahiyar Amurka inda aka samu sabbin wadanda suka kamu da cutar 129,772, a cewar hukumar WHO, hukumar ta kara cewa, kusan rabin sabbin adadin wadanda suka kamu da cutar an same su ne a kasashen Amurka da Brazil, wanda ya kai 53,213 da kuma 48,105, a kasashen biyu.

Yankin kudu maso gabashin Asiya shi ne waje na biyu mafi yawan mutanen da suka kamu da cutar da adadin sabbin masu kamuwa da cutar 27,947 da kuma mutane 534 da suka mutu cikin sa'o'i 24 a sanadiyyar cutar.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China