Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tsang Kwok Wai Erick: Dole a gufanar da masu tayar da tarzoma a HK a gaban kuliya
2020-06-27 15:57:11        cri

Shugaban hukumar kula da gyaran fuska kan tsarin Hong Kong da harkokin babban yankin kasar Sin ta yankin musamman na Hong Kong Tsang Kwok Wai Erick ya zanta da wakilin CMG jiya, inda ya bayyana cewa, ya dade yana jiran kafuwar dokar tsaron kasa ta Hong Kong, saboda kafuwar dokar ta nuna cewa, gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali kan yankin, kuma za ta tsorata masu tayar da tarzoma a yankin, a sanadin haka za a kara tabbatar da kwanciyar hankali da dadin rayuwar al'ummun yankin.

Jami'in ya kara da cewa, yanzu haka an tayar da tarzoma a Hong Kong, amma gwamnatin kasar Sin ta yi hakuri matuka kan batun, yana mai cewa, idan tarzomar ta kawo hadari ga tsaron kasa, to tabbas gwamnatin za ta dauki matakin da ya wajaba bisa dokokin da abin ya shafa, domin gwamnatin kasar Sin tana sauke nauyin dake wuyanta yayin da take daidaita harkokin Hong Kong, tare kuma da nuna kulawa ga yankin bisa manufar "kasa daya mai tsarin mulki biyu."(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China