Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin Sin: Ya kamata a tallafawa al'amurran ci gaban Somaliya
2019-08-22 10:49:33        cri

Wakilin kasar Sin a MDD ya ce, ya kamata kasashen duniya su ci gaba da tallafawa Somaliya wajen karfafa matsayin gwamnatin kasar.

Wu Haitao, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, ya ce duk da irin ci gaban da aka samu a baya bayan nan, amma yanayin da ake ciki a kasar ta gabashin Afrika yana da matukar sarkakiya, kana yanayin zaman lafiya da kwanciyar hankalin kasar yana fuskantar kalubaloli masu yawa.

Wu ya bukaci al'ummar kasa da kasa su taimaka wajen inganta harkokin gwamnatin tarayyar kasar, da kuma kyautata dangantakar dake tsakanin gwamnatin tsakiya da sauran gwamnatocin jihohin kasar.

Kamata ya yi dukkan mambobin gwamnatin jihohin kasar Somaliya, su martaba ruhun hadin gwiwa, su mutunta matsayin gwamnatin tarayya, kana su yi hadin gwiwa tare domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da ma ci gaban kasar.

Wu ya kara da cewa, ya kamata kasashen duniya su ci gaba da taimakawa kasar Somaliya wajen karfafa matsayin tabbatar da al'amurran tsaron kasar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China