Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin Sin zai kafa masana'antar harhada taragun jirgin kasa a Najeriya
2019-11-10 16:16:52        cri
Babban kamfanin gine gine na kasar Sin ko CCECC a takaice, ya aza tubalin gina masana'antar harhada taragun jiragen kasa a garin Kajola na jihar Ogun dake kudancin Najeriya, a wani mataki na tallafawa shirin kasar na zamanantar da fannin sufurin jiragen kasa.

Yayin bikin aza harsashin ginin kamfanin wanda ya gudana a jiya Asabar, mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo, ya bayyana taron a matsayin mai cike da tarihi. Mr. Osinbajo ya ce da zatar an kammala aikin, masana'antar za ta rika samar da ratagun jiragen kasa, ciki hadda wadanda za a yi amfani da su a layin dogo na Lagos zuwa Ibadan, da Abuja zuwa Kaduna, baya ga sauran kasuwannin yankunan Afirka da za su bukace su.

A nasa tsokaci, ministan sufurin Najeriya Rotimi Amaechi, ya ce masana'antar ita ce irin ta ta farko da za a gina a kasar, za kuma ta samar da guraben ayyukan yi kimanin 5,000.

Shi kuwa babban jami'i mai lura da harkokin tattalin arziki da cinikayya na ofishin jakadancin Sin dake Najeriya Li Yuan, alkawari ya yi na karfafawa kamfanonin Sin gwiwar zuba jari a Najeriya, musamman a fannonin sarrafa hajoji da noma. Ya ce yawan jarin kai tsaye da Sin ke zubawa a Najeriya a fannonin sarrafa hajoji ya karu zuwa dalar Amurka biliyan 3, matakin da ya samar da karin dubban guraben ayyukan yi ga al'ummun da ake kafa masana'antun a yankunan su. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China