Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta kaddamar da sabon gangamin yaki da bayanan karya
2020-07-01 13:15:14        cri

MDD ta kaddamar da wani sabon gangami jiya Talata, ta hanyar canja halayyar jama'a, biyo bayan barazanar bayanan karya dake karuwa a kafar Intanet, musamman kan cutar COVID-19.

Gangamin mai suna "ka dan dakata", a fadawa masu amfani da Intanet su yi tunani game da abin da suke kokarin rabawa kafin su watsa a Intanet.

Da yake Karin haske cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya ce, bayanan karya game da cutar COVID-19 na bazuwa kamar wutar daji, yana kuma yin babbar barazana ga lafiyar al'umma ta hanyar illata matakan kimiyya da ake dauka. Yana mai cewa, wasu ne suka tsara da nufin ci da gumin mu a lokacin da duniya ke cikin fargaba.

Amma jami'in na MDD ya ce, akwai hanyoyi da masu amfani da kafar Intanet za su gane bayanan karya da ma dakile yaduwarsu. Burin mu a cewarsa shi ne, a dan dakata, kula kafin ka raba bayani, kasance mai bin sabon tsarin al'umma.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China