Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya kamata a shawo kan matsalar yan gudun hijira ta hanyoyi da matakai daban daban, in ji jakadan Sin
2020-06-19 10:44:46        cri

Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Yao Shaojun, ya ce kamata ya yi daukacin sassan masu ruwa da tsaki, su zage damtse wajen aiwatar da matakan warware matsalolin da 'yan gudun hijira ke fuskanta, ta hanyar dabaru da tsare-tsare masu nagarta, tare da magance tushen kwararar 'yan gudun hijirar.

Yao Shaojun, ya ce matsalar 'yan gudun hijira ta shafi duniya ne gaba daya, don haka tana bukatar daukacin kasashen duniya su hada kai wajen shawo kan ta. Ya ce akwai bukatar kasashen duniya su kyautata hadin kai, da karfafa rawar da hukumomin kasa da kasa, kamar hukumar 'yan gudun hijira ta MDD UNHCR ke takawa.

Mr. Yao na wannan tsokaci ne, yayin taron kwamitin tsaron MDD da ya gudana ta kafar bidiyo a jiya Alhamis. Jami'in ya ce mafi yawan 'yan gudun hijira na fitowa daga yankunan dake fama da tashe-tashen hankula dake cikin ajandar kwamitin na tsaro. Ya ce "Ya zama wajibi a aiwatar da cikakkun manufofi da za su haifar da zaman lafiya da ci gaba. Kaza lika akwai bukatar zuba jari a fannin dakile tashe-tashen hankula da salhu, da samar da zaman lafiya, da yaki da talauci da wanzar da ci gaba. Ta haka ne a cewar jami'in, za a iya samar da yanayi na hakika, da zai ba da damar mayar da 'yan gudun hijira zuwa ga kyakkyawan yanayin zaman lafiya da lumana a kasashensu na asali. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China