Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Antonio Guterres ya yi kira da a hada kai a dukkanin fannoni don yaki da kalubalen COVID-19
2020-06-26 11:22:02        cri
Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya yi kira ga kasashen duniya, da su yi hadin gwiwa, da cudanya da juna daga dukkanin fannoni, wajen shawo kan kalubalen lafiya dake addabar sassan duniya, sakamakon yaduwar cutar numfashi ta COVID-19.

Mr. Guterres wanda ya yi wannan kira, yayin ganawarsa da manema labarai ta kafar bidiyo a jiya Alhamis, yayin kaddamar da cikakken shirin MDD na yaki da COVID-19, ya ce ya zama wajibi dukkanin sassan MDD, da na hukumomin yankunan duniya, da cibiyoyin hada-hadar kudade na kasa da kasa su hada karfi da karfe, wajen shawo kan matsalolin da wannan annoba ta haifar.

Jami'in ya ce cudanyar dukkanin sassa na iya zama managarcin ginshikin tsarin gudanarwa a duk inda aka bukaci hakan.

Guterres ya kara da cewa, kalubalen da kasashen duniya ke fuskanta na da yawa, kama daga cutar COVID-19, da sauyin yanayi, zuwa batun nuna wariyar launin fata da rashin daidaito tsakanin al'umma.

Daga nan sai ya jaddada bukatar dake akwai ga shugabannin duniya, da su yi hangen nesa, tare da rungumar salon hadin kai, duba da muhimmancin sa ga rayuwar daukacin bil Adama, musamman a wannan gaba da duniya ke cikin wani mawuyacin yanayi. (SAMINU)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China