Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Alkaluman tattalin arzikin Afrika ta kudu sun sauka da kaso 2.3 cikin rubu'in farko na bana
2020-07-01 10:43:00        cri

Babban jami'in kididdiga na kasar Afrika ta kudu, Risenga Maluleke, ya ce alkaluman GDP na kasar, sun ragu da kaso 2.3 bisa dari a rubu'in farko na bana.

A cewar rahoton hukumar kididdiga ta kasar, raguwar GDPn a rubu'in farko na bana, shi ne karo na 3 a jere, bayan raguwar da ya yi da kaso 0.6 bisa dari a rubu'i na 3 na shekarar 2019 da kuma kaso 1.4 bisa dari a rubu'i na 4 na shekarar.

Rahoton hukumar ya nuna cewa, bangarorin hakar ma'adinai da na kera kayayyaki, na daga cikin bangarorin da suka ba da gudunmuwa ga raguwar GDPn. Sauran wasu bangarori ma sun ragu saboda raguwar bukatu.

Shugabar tsangayar nazarin kimiyyar tattalin arziki da kasuwanci ta jami'ar Witwatersrand, Jannie Rossouw, ta shaidawa Xinhua cewa, za a ci gaba da samun raguwar a rubu'i na 2 na bana, bisa la'akari da tasirin matakan kulle.

Kakakin kungiyar kwadago ta kasar Sizwe Pamla, shi ma ya ce idan gwamnati ta gaza zuba kudi domin farfado da tattalin arziki, to ba zai samu ci gaba ba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China