Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mataimakin shugaban Sin ya tattauna da takwaransa na Afirka ta kudu
2019-10-31 20:16:35        cri

Mataimakin shugaban kasar Sin Wang Qishan, a yau Alhamis ya tattauna da takwaransa na kasar Afirka ta kudu David Mabuza tare da jagorantar cikakken zama na 7 na hukumar raya alakar kasashen biyu tare a nan birnin Beijing.

Wang ya ce, hukumar raya alakar kasashen biyu, ta taka muhimmiyar rawa wajen zurfafa alaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen biyu, yana mai kira ga sassan biyu, da su kara mutunta juna a fannin siyasa, da goyawa muradun juna da manyan batutuwan dake shafar su baya, more damammakin ci gaba tare, da karfafa musaya tsakanin al'ummominsu da musayar al'adu da aiki tare wajen kare alakar bangarori daban-daban gami da muradun kasashe masu tasowa.

Jami'in na kasar Sin, ya kuma yi kira ga kasashen Sin da Afirka ta kudu da sauran kasashen Afirka, da su bullo da dabarun raya kasa, yana mai cewa, kasar Sin za ta ci gaba da hada kai da Afirka ta kudu, don ingiza alakar Sin da Afirka bisa manyan tsare-tsare zuwa wani sabon mataki, da gina al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya tsakanin kasashen Sin da Afirka.

A nasa bangare, Mabuza ya taya jamhuriyar jama'ar kasar Sin murnar cika shekaru 70 da kafuwa, yana mai cewa, bangaren Afirka ta kudu, yana fatan karfafa alaka da kasar Sin a harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya, zai kuma nazarci tare da daukar batutuwan da suka shafi bangaren kasar Sin ta hanyar da za ta dace da raya alakar kasashen biyu.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China