Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An mika makamai sama da 1,400 ga jami'an tsaro a Afirka ta kudu
2020-01-01 14:55:19        cri

Rundunar 'yan sandan kasar Afirka ta kudu, ta ce ta karbi bindigogi 1,465 da kuma albarusai 14,861, daga hannun fararen hular kasar, karkashin wani shiri na raba al'umma da muggan makamai, da kuma yafiya da gwamnati ta tsara.

An dai kaddamar da wannan aiki ne a ranar 1 ga watan Disambar shekarar 2019. Rundunar 'yan sandan ta ce daukacin wadanda suka mika makaman da suka mallaka ba tare da izini ba, za su samu yafiya, muddin sun yi hakan nan da karshen wa'adin aikin, wato ranar 31 ga watan Mayun shekarar nan ta 2020.

Da yake tsokaci game da wannan batu, kakakin rundunar 'yan sandan kasar Vishnu Naidoo, ya ce abu ne mai karfafa gwiwa, ganin yawan bindigogi da albarusai da mutane suka mika ga hukuma, duba da cewa, irin wadannan makamai ne ake amfani da su yayin aikata muggan laifuka, da ma duk lokacin da wani hargitsi ya auku.

Jami'in ya kara da cewa, daukacin makaman da za a tattara bayan kammala shirin na yin afuwa, za a yi gwajin su, domin tabbatar da ko an taba amfani da su yayin wasu laifuka, kafin a dauki matakin karshe na lalata su. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China