Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban AU ya yi kira ga sojojin Afrika ta Kudu su taimaka wajen kawar da makamai a Afrika
2020-02-22 15:42:16        cri

Shugaban Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya yi kira ga rundunar sojin kasar, su taimaki nahiyar wajen cimma burinta na kawar da makamai.

Cyril Ramaphosa, ya yi wannan kira ne yayin da yake jawabi ga rundunar sojin kasar a yayin bikin ranar tunawa da sojoji a garin Polokwane.

Ya tunawa sojojin cewa, ana bikin wannan rana ne a lokacin da kasar ta karbi ragamar shugabancin Tarayyar Afrika AU.

Shugaba Ramaphosa ya kara da cewa, Afrika ta Kudu na sa ran rundunar sojin za ta taimaka mata wajen sauke nauyin dake wuyanta a fannin cimma zaman lafiya da tsaron nahiyar. Ya ce a matsayin rundunar ta wadda MDD da AU suka dorawa nauyin inganta tsaro a nahiyar, suna sa ran za ta sauke nauyin dake wuyanta. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China