Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
IMF: Tattalin arzikin kasashen Afirka dake yankin kudu da Sahara zai ragu da kaso 3.2 a shekarar 2020
2020-06-30 13:01:24        cri

Wani sabon rahoto da asusun ba da lamuni na duniya (IMF) ya fitar a jiya Litinin, ya yi hasashen cewa, tattalin arzikin kasashen Afirka dake yankin kudu da hamadar Sahara, zai ragu da kaso 3.2 cikin 100 a wannan shekara. A daidai gabar da annobar ke ci gaba da yin illa ga bangaren lafiya da tattalin arziki, tasirin da galibi ke shafar kasashe matalauta.

Darekta asusun mai kula da sashen Afirka, Abebe Aemro Selassie, ya bayyana cewa, har yanzu annobar COVID-19 na kololowarta a wannan yankin. Kuma abu mafi muhimmanci a halin yanzu, shi ne kokarin kare rayuka da daukar matakan inganta tsarin kiwon lafiya da hana yaduwar cutar.

Selassie ya ce, akwai bukatar kasashen duniya su gaggauta cika alkawuran da suka yi na ba da taimako, yana mai cewa, har yanzu kasashen dake yankin, ba su samu tallafin sama da dala biliyan 110 da wasu karin daa biliyan 44 da aka yi musu ba.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China