Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin da Habasha sun amince da karfafa dangantaka tsakanin Sin da Afrika a yaki da COVID-19
2020-06-30 10:52:55        cri

Mamban majalisar gudanarwar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya tattauna ta wayar tarho da ministan harkokin wajen Habasha, Gedu Andargachew, inda bangarorin biyu suka amince da karfafa dangantaka da hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika wajen yaki da annobar COVID-19.

Wang Yi ya nanata cewa, a shirye Sin take ta yi aiki da kawayenta na Afrika, ciki har da Habasha, domin aiwatar da sakamakon taron da bangarorin biyu suka yi kan yaki da COVID-19.

Ya ce na farko, Sin za ta ci gaba da samar da taimakon gaggawa ga kasashen Afrika. Na biyu, za ta inganta aiwatar da sakamakon da aka cimma yayin taro da aka yi a Beijing, kan hadin gwiwar bangarorin biyu. Na uku, ya kamata a fara ginin hedkwatar cibiyar dakile yaduwar cututtuka da kandagarkinsu ta Afrika kafin karshen bana. Na hudu, ya ce kasar Sin za ta gaggauta tattaunawa da kasashen Afrika da nufin aiwatar da shirin kungiyar kasashen G20 na dakatar da biyan bashi.

A nasa bangaren, Gedu ya taya Sin murna dangane da nasarar taron da ta yi da kasasehn Afrika kan yaki da COVID-19 da kuma taron manyan jami'ai da aka yi ta kafar bidiyo kan hadin gwiwar kasa da kasa karkashin shawarar ziri daya da hanya daya, wanda ya nuna aniyar Sin ta hada hannu da kasashen duniya wajen yaki da COVID-19. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China