Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hadin gwiwar Sin da Habasha na da muhimmanci wajen cimma burin Habasha na sauya tsarin tattalin arzikinta
2020-01-04 16:13:44        cri

Yayin da kasar Habasha ta fara gagarumin garambawul ga tsarin tattalin arzikinta da ake kira Homegrown Economic Reform Program, dake da burin kawar da rashin daidaito a bangarorin tattalin arziki da kuma aza tubulin samar da ci gaba mai dorewa ta ko wace fuska, kwararru sun jadadda muhimmiyar rawar da kyautata dangantakar Sin da Habasha za ta yi wajen cimma burin shirin.

Costantinos Bt. Costantinos, wanda ya taba zama mai ba da shawara kan harkokin tattalin arziki ga Tarayyar Afrika AU da kuma hukumar kula da tattalin arzikin nahiyar Afrika ta MDD, ya shaidawa Xinhua cewa, Habasha tana samun ci gaban tattalin arziki cikin 'yan shekarun da suka gabata. Sai dai, yanzu haka, kasar na fuskantar hauhawar farashin kayayyaki, da karuwar tsadar rayuwa da karancin kudaden ketare, kuma gudunmuwar kasar Sin, muhimmiya ce ga shirin sauya tsarin tattalin arzikin kasar domin samun ci gaba mai dorewa.

Ya ce kasar Sin za ta iya taimakawa Habasha wajen sauya manufofin tattalin arziki domin inganta samun kudin shiga da shirin karfafa ayyukan bangarori masu zaman kansu, da gwamnati ta bullo da shi domin shawo kan matsaloli da kara habaka tattalin arzikin kasar.

Constantinos, wanda farfesa ne a jami'ar Habasha dake Addis Ababa, ya kara da jadadda bukatar gwamnatin Habasha, ta yi koyi da gogewar kasar Sin, wajen fatattakar cin hanci, yana mai bayyana cin hanci a matsayin babban abun dake tarnaki ga cimma manyan burikan shirin yi wa tsarin tattalin arzikin kasar garambawul. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China