Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
IMF zai tallafawa shirin sauya salon bunkasa tattalin arzikin Habasha
2019-12-25 11:00:29        cri
Asusun ba da lamuni na IMF, ya sha alwashin tallafawa shirin sauya salon bunkasa tattalin arzikin kasar Habasha, wanda ya kunshi kawar da rashin daidaito tsakanin sassan tattalin arziki, da kafa ginshikin ci gaba mai dorewa a dukkanin sassa.

A makon da ya gabata ne dai asusun na IMF, ya amince da samar da kudi da yawan su ya kai dalar Amurka biliyan 2.9 ga kasar. A jiya Talata kuma, ya sanar da cewa, tallafin wani mataki ne na goyon bayan kudurorin gwamnatin Habashar na sauka alakar tattalin arzikin kasar.

Cikin wani rahoton nazarin makomar Habashan, wanda asusun na IMF ya fitar, ya ce mahukuntan Habasha sun tsara managarcin salon bunkasa tattalin arziki mai dacewa da yanayin da kasar ke ciki. Suna kuma tattaunawa da dukkanin sassa masu ruwa da tsaki a fannin raya tattalin arziki, sun kuma fara aiwatar da matakan cimma nasarar kudurorin da suka sanya gaba.

Har ila yau asusun na IMF, ya ce baya ga dakile karancin kudaden musaya na kasar da wannan manufa za ta haifar, a hannu guda kuma, hakan zai yiwa kasar kandagarki ga nauyin bashi. Bugu da kari, matakin zai kawo managarcin sauyi a fannin hada hadar kudin kasar, da samar da karin kudaden haraji, idan har an samu tallafin kwarewa da sanin makamar aiki, da horas da ma'aikata.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China