Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Habasha ta ce tana gudanar da aikin share fagen taron kolin AU dake tafe
2019-12-29 15:59:34        cri

Gwamnatin kasar Habasha ta sanar cewa, shirye shirye sun yi nisa domin karbar bakuncin taron kolin kungiyar tarayyar Afrika AU karo na 33 wanda za'a gudanar tsakanin 21 ga watan Janairu zuwa 10 ga watan Fabrairu, a helkwatar kungiyar AU dake Addis Ababa, babban birnin kasar.

Taron kolin shugabannin kasashen Afrika, zai gudana karkashin taron majalisar wakilan kasashen Afrika karo 33, zai tattara shugabannin na Afrika a birnin Addis Ababa daga ranar 9 zuwa 10 ga watan Fabrairu. Taken taron kolin shi ne, "Kawar da amon bindiga: Samar da ingantaccen yanayin zaman lafiya da ci gaban Afrika."

A ranar Asabar, ma'aikatar harkokin wajen kasar Habasha ta sanar cewa, kwamitin da kasar ta kafa, wanda ya kunshi dukkan masu ruwa da tsaki, yana ci gaba da gudanar da aikinsa ba kakkautawa domin cimma nasarar gudanar da taron kolin.

A halin yanzu kwamitin yana gudanar da muhimman ayyuka, da suka hada da shirya tsarin sufuri, samar da tsaro, da tanadin otel otel ga baki, da kuma sauran ayyukan da suka shafi saukar baki.

Hukumar gudanarwar AU ta sha nanata aniyarta ta daukar kwararan matakan kawo karshen amon bindiga a nahiyar a shekarar 2020, musamman wajen amfani da matakan shawon kan matsalar tun daga tushe da kuma yunkurin tabbatar da bunkasuwar ci gaban tattalin arzikin nahiyar da zamantakewar al'umma.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China