Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Me ya sa tattalin arzikin Sin ke iya samun farfadowa cikin sauri?
2020-06-28 20:15:43        cri

Wasu alkaluman da ma'aikatar al'adu da yawon shakatawa ta kasar Sin ta gabatar a jiya Asabar sun nuna cewa, cikin lokacin hutu na kwanaki 3 da aka yi a kasar, a sabili da bikin Duanwu na gargajiya, an samu karbar baki masu yawon shakatawa kusan miliyan 49 a kasar, adadin da ya kai kaso 50.9% bisa na shekarar bara. Kana yawan kudin da aka samu a fannin yawon shakatawa a cikin wannan wa'adi ya kai Yuan biliyan 12 da wani abu, jimillar da ta koma wani matsayi na kaso 31.2% bisa na shekarar da ta gabata. Wadannan alkaluman sun nuna yadda tattalin arzikin kasar ke samun farfadowa cikin sauri.

A wannan shekarar da muke ciki, annobar COVID-19 ta haifar da babbar illa ga harkokin kasuwannin kasar Sin. Amma bisa ci gaban da aka samu a fannin hana yaduwar cutar, ayyukan sayayya su ma na samun farfadowa yadda ake bukata, har ma ana ci gaba da kokarin inganta ayyukan sayayya a kasar, wadanda suka habaka zuwa fannonin yawon shakatawa, da al'adu, da makamantansu.

Bisa hasashen da asusun bada lamuni na duniya IMF ya yi, daga cikin manyan tattalin arzikin duniya, kasar Sin ita kadai ke iya kiyaye wani yanayi na karuwa a fannin tattalin arziki a shekarar 2020 da muke ciki. Wannan hasashen ya sa kamfanonin kasashe daban daban ke kokarin habaka hadin gwiwarsu da kasar Sin. Misali, a bikin bajekolin kayayyakin shigi da fici karon 127 da ya gudana a Guangzhou dake kudancin kasar Sin, a kwanakin baya, wasu 'yan kasuwa da suka zo daga kasashe da yankuna 217 sun halarci bikin.

Me ya sa tattalin arzikin Sin ke iya samun farfadowa cikin sauri daga mawuyacin halin da ake ciki na fama da cutar COVID-19? Wasu manazartar al'amuran duniya na ganin cewa, yayin da ake fuskantar annobar COVID-19, jam'iyya mai mulki da gwamnatin kasar sun mai da tsaron lafiyar jama'a a gaban kome, inda suka jagoranci aikin dakile cutar da farfado da ayyukan masana'antu cikin kima, lamarin da ya tabbatar da damar farfadowar tattalin arzikin kasar cikin kankanin lokaci.

Ban da wannan kuma, yanayin samun ci gaban tattalin arzikin kasar bai taba canzawa ba, inda yawan al'ummar kasar su biliyan 1.4 ya tabbatar da samun cikakkun bukatu a gida, sa'an nan wani ingantaccen tsarin masana'antu da ya shafi fannoni daban daban, da fasahohin zamani, da dimbin kwararru a fannoni daban daban, sun sa kasar Sin ka iya yin takara da sauran manyan kasashe a fannin janyo jarin da ake bukata don raya tattalin arziki.

Wadannan dalilai sun sanya ana da imanin cewar, Sinawa za su haye wahalhalun da suke fuskanta a halin yanzu, inda za su kara ciyar da tattalin arzikin kasarsu zuwa gaba, gami da taimakawa wajen samun ci gaban tattalin arzikin duniya. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China