Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Takardar bayanai: Sin ta taka rawar gani a yaki da cutar COVID-19
2020-06-08 17:10:47        cri

Masu hikimar magana na cewa himma ba ta ga raggo, wannan batu haka yake, domin kuwa tun bayan samun rahoton barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19 a birnin Wuhan na lardin Hubei, mahukuntan kasar Sin suka tsaya tsayin daka ba dare ba rana wajen tinkarar matsalar ba tare da kakkautawa ba, lallai al'ummar Sinawa sun nuna halayyar musamman na zama tsintsiya madaurinki daya domin tinkarar annobar don a gudu tare a tsira tare kamar yadda masu hikimar magana ke cewa hannu daya ba ya daukar jinka. Wannan halayya ta nuna da'a da biyayya wanda dukkan Sinawa suka nuna, lallai ya haifar da mai ido domin kuwa wannan ne ya bayar da nasarar da kasar ta cimma tun bayan barkewar cutar a farkon wannnan shekara. Wannan ne ma ya sa a ranar Lahadin da ta gabata, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gabatar da wata takardar bayani dangane da nasarori da matakan da kasar ta dauka na yaki da cutar COVID-19 tare da yin cikakkun bayanai game da irin wahalhalun da kasar Sin ta haye, da jerin muhimman matakan da kasar ta dauka domin dakile yaduwar cutar gami da aikin jinyar wadanda suka kamu da cutar, musamman, game da kokarin hadin gwiwa da bangarori daban daban don warware wannan babban batun lafiya wanda a halin yanzu ya zama batun kiwon lafiya da duk duniya ke tsaka da fuskanta. Wannan batu al'amari ne a bayyane dangane da yadda mahukuntan kasar Sin suka tinkari ibtila'in wanda a halin yanzu ya zama tamkar ruwan dare game duniya duba da yadda annobar ke ci gaba da yaduwa a duk duniya baki daya. Ko da yake salon da kasar Sin ta yi amfani da shi wajen tinkarar annobar ya zama tamkar abin koyi ga sauran kasashen duniya domin kuwa ya kasance salo ne na bai daya wato dukkan jami'an gwamnatin kasar, hukumomin gwamnatin, har ma da hukumomi masu zaman kansu gami da daidaikun jama'a sun hada karfi da karfe wajen tinkarar annobar. Alal misali, tun bayan barkewar cutar ta COVID-19 a kasar, babban sakataren jam'iyyar Kwaminis ta kasar, kana shugaba Xi Jinping, shi da kansa, ya jagoranci aikin dakile cutar inda ya jaddada bukatar maida rayuka da lafiyar jikin jama'a a gaban komai. Wadannan kalamai na shugaban kan batun mayar da kula da lafiyar jama'a a gaban komai, hakika, ya yi gagarumin tasiri a yaki da annobar, domin matakin ya baiwa al'ummar kasar kwarin gwiwa wajen bada cikakken hadin kai da kuma shiga a dama da su kamar yadda masu hikimar magana ke cewa "daga na gaba ake gane zurfin ruwa" wannan ya sa al'ummar Sinawa sun kara sadaukar da kai da ba da hadin kai domin fuskantar wahalhalu tare. Irin wadannan matakai na babu babba ba yaro wanda kowane Basine ya bayar tasa gudunmawar gwargwadon hali domin ganin an kai ga kaci ya taimaka matuka wajen ganin kwalliya ta biya kudin sanulu. Hakika, wannan salo da dabaru da Sin ta yi amfani da su sun taimakawa kasar wajen samun nasarar kandagarki da hana yaduwar annobar COVID-19 cikin kankanin lokaci. Ko shakka babu matakan da Sin ta dauka wajen dakile annobar ya haifar da sakamako mai gamsarwa domin da ma an ce "hannu da yawa maganin kazamar miya". (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China