Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Aiki ga mai kare ka
2020-06-10 17:31:17        cri

Yanzu dai Sinawa sun kara tabbatar wa duniya cewa, duk abin da suka sanya a gaba, to hakika za su aiwatar da shi cikin nasara, kamar yadda suka gabata bayan annobar COVID-19, har suka raba fasahohi da jami'an kiwon lafiya da ma kayayyakin yaki da wannan annoba ga sauran kasashen duniya. Baya ga kokarin da masanan lafiyar kasar ke yi na samar da alluran rigakafi da maganin cutar.

Wani labarin mai dadin ji shi ne, kasar Sin tana kan hanyar kammala shirin da ta tsara na kawar da kangin talauci a fadin kasar cikin shekarar 2020 da muke ciki, da sauran manufofi da tsare-tsare da nufin raya tattalin arziki da zamantakewar al'ummar Sinawa da ma duniya baki daya.

Wata babbar nasara ta baya-bayan nan, ita ce yadda birnin Wuhan dake lardin Hubei a yankin tsakiyar kasar Sin ya yi nasarar yiwa mazauna birnin kimanin miliyan 10 gwajin cutar COVID-19 cikin kwanaki 19 don tantance masu dauke da cutar.

Alkaluma sun ce, daga ranar 14 ga watan Mayu zuwa 1 ga watan Yuni, an yi wa mazauna birnin 9,899,828 gwajin cutar. A hannu guda kuma, an yi nasarar killace mutane 300 da suka kamu da cutar kuma suka warke ba tare da nuna alamu ba. Baya ga dukkan mutane 1,174 da aka tabbatar sun yi mu'amula da wadanda aka gwada ba su da alamun cutar. Masu iya magana na cewa, idan da Zafi-Zafi kan bugi Karfe.

Shi dai wannan gwaji da aka yi kyauta ne, ma'ana gwamnati ce za ta biya dukkan kudaden. Yanzu haka birnin na Wuhan ya kashe Yuan miliyan 900, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 126 wajen yin gwaje-gwaje, matakin da ya baiwa mazauna birnin da ma kasar Sin baki daya tabbaci, baya ga taimakawa birnin wajen dawo da harkokin tattalin arziki da zamantakewa kamar yadda suke a baya.

Hakan ya kara tabbatar da kalaman shugaban kasar Sin Xi Jinping na ba da muhimmanci ga batun da ya shafi jama'a. wato "Jama'a su ne Kasuwa ba Tarin Rumfuna ba". Wannan ne ya sa mahukuntan kasar Sin ta fitar da takardar bayani game da matakan da suka dauka na yaki da CIVID-19, ta yadda duniya za ta kara fahimtar wahalhalu da bayanai da dabarun da ta fitar kan yaki da wannan annoba, har ma ta kasance kasa ta farko a duniya da ta yi nasara ganin bayan wannnan cuta. (Marubuci: Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China