Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hukumomin Sudan za su koyi darasi daga nasarorin Sin a yaki da COVID-19
2020-06-15 19:48:04        cri

Yayin da kasashen duniya ke cigaba da kokarin dakile annobar cutar sarkewar numfashi ta COVID-19 wacce a halin yanzu ta zama babban kalubalen lafiya wanda ya sha gaban shugabanin kasashe da hukumonin lafiya na kasa da kasa. Annobar ta yi matukar ta'azzara musamman bisa yadda daukacin bil adama ke fama da wahalhalun matsin rayuwa da komadar tattalin arziki saboda matakai daban daban da shugabannin kasashe da hukumomi ke dauka a matsayin dabarun dakile yaduwar cutar a kasashen duniya. Kasar Sin wacce ta fara fuskantar radadin annobar tun bayan barkewar cutar a yankin Wuhan, sai dai kuma, kasar ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen daukar kwararan matakan da suka dace domin yin kandagarki da kuma dakile bazuwar cutar gami da bada kulawa ga mutanen da suka kamu da cutar. Sannu a hankali kwalliya ta biya kudin sabulu, kasar Sin ta samu manyan nasarori a yaki da annobar ta COVID-19 tun kusan watanni ukun farko bayan barkewar annobar.

Nasarorin da kasar ta samu ya yi matukar daukar hankalin kasa da kasa, inda hakan ne ma tasa gwamnatin kasar Sudan ta yanke shawarar koyon darasi daga irin nasarorin da kasar Sin ta samu a yaki da annobar kamar yadda masu hikimar magana ke cewa daga na gaba ake gane zurfin ruwa. Wani babban jami'in kasar Sudan ya sanar cewa, nasarorin da kasar Sin ta samu wajen dakile annobar COVID-19 za su kasance a matsayin manyan darrusan da kasar za ta yi amfani da su domin dakile annobar a kasar. A sanarwar da majalisar shugabancin kasar Sudan ta fitar ta bakin wani mamban majalisar gudanarwar kasar ta Sudan, kana shugaban babban kwamitin ayyukan lafiyar gaggawa na kasar. Jami'in na Sudan ya yi wannan tsokaci ne a lokacin ganawa da tawagar kwararrun likitocin kasar Sin da suka ziyarci kasar domin taimaka mata a kokarin dakile annobar. Hukumomin kasar ta Sudan sun yi amana cewa nasarorin da kasar Sin ta samu wajen dakile annobar COVID-19 za su yi matukar taimakawa kasar Sudan, yayin da kasar za ta yi amfani da nasarorin na Sin a matsayin abin koyi a kokarin kawar da annobar.

Wani abin alfahari dai shi ne, jami'in da ya shugabanci tawagar kwararrun masana lafiyar kasar Sin da suka ziyarci Sudan don marawa kasar baya a yunkurin dakile annobar ya yi nuni da cewa, burin da Sudan ke son cimmawa zai kai ga nasara kasancewar kwararrun na kasar Sin sun yi musayar kwarewa da takwarorinsu na kasar Sudan a bangarorin bincike game da cutur, da aikin jiyya, da kandagarkin annobar, kana da kuma yadda za'a dakile cutar cikin kankanin lokaci. Kuma wannan ke nuna cewa lallai tamkar kaya ne ya kwance a gindin kaba kamar yadda masu hikimar magana ke cewa abin nema ya samu wai matar makadi ta haifi ganga. Fatan da ake da shi shi ne kasa da kasa su yi hadin gwiwa da yin koyi da juna da nufin kawo karshen annobar ta COVID-19 wacce a halin yanzu ta gigita daukacin kasashen duniya. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China