Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An rufe bikin baje kolin Canton Fair karo na 127 ta yanar gizo
2020-06-25 16:15:04        cri

A ranar 24 ga wata aka rufe bikin baje kolin hajojin da ake shigowa da su kasar Sin, da wadanda ake fitarwa daga kasar da aka fi sani da "Canton Fair" karo na 127 ta yanar gizo, inda aka gudanar da harkokin cinikayya yayin bikin da aka shirya ta yanar gizo a karo na farko yadda ya kamata, Bikin ya jawo hankalin 'yan kasuwa masu sayen kayayyaki dake kasashe da shiyyoyi da yawansu ya kai 217, adadin ya kai matsayin koli a tarihi.

Jami'in watsa labarai na bikin Xu Bing ya bayyana cewa, kamfanonin kasar Sin da na kasashen ketare sama da dubu 26 sun yi nune-nunen kayayyaki ba rana ba dare a cikin kwanaki 10 da suka gabata, sakamakon da aka samu yayin bikin ta yanar gizo zai sa kaimi kan samun jari waje da cinikayyar waje a kasar Sin, kana zai nuna wa kasa da kasa manufar kasar Sin ta kara bude kofa ga ketare.

Yayin bikin, an nuna hajoji sama da miliyan 1 da dubu 800 ta kafar bidiyo kai tsaye, ana iya cewa, bikin Canton Fair na wannan karo zai ingiza ci gaban cinikayyar kasa da kasa ta hanyar daukar hakikanin matakai.

Shugaban kamfanin cudanyar al'adu da bayanai na kasar Sin dake kasar Kenya Gao Wei yana mai cewa, bana kamfanonin Kenya suna bukatar kayayyaki masu yawa, sakamakon barkewar annobar cutar COVID-19, a don haka shi kansa yana tuntubar 'yan kasuwa masu sayen kayayyaki na kasar sama da 60 domin samar musu da kayayyaki.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China