Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Musulman Sin ba za su je aikin Hajjin bana ba saboda COVID-19
2020-06-25 15:32:45        cri

Kungiyar musulmai ta kasar Sin ta sanar a jiya Laraba cewa, musulman kasar ba za su je aikin Hajjin bana ba, saboda cutar COVID-19 da har yanzu duniya ke fama da ita.

Wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta bayyana cewa, duk da nasarar da kasar Sin ta samu wajen yaki da wannan annoba, har yanzu cutar na yaduwa a wasu sassan duniya, kana ba a shawo kanta ba, don haka ne, ta yanke wannan shawara.

A ranar Litinin ne, kasar Saudiya ta sanar da cewa, maniyatta dake cikin kasar ce kadai, za a bari su yi aikin Hajjin na bana, saboda matsalar cutar COVID-19.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China