2020-06-15 20:23:12 cri |
An kaddamar da baje kolin wanda aka shafe gwamman shekaru ana gudanarwa ne daga birnin Guangzhou fadar mulkin lardin Guangdong.
A bana bikin baje kolin wanda za a shafe kwanaki 10 ana gudanarwa, ya samu mahalarta kamfanoni 25,000, daga sassan sayar da hajoji 16, da suka kunshi nau'o'in hajoji miliyan 1.8.
Tun a shekarar 1957 ne aka fara gudanar da bikin baje kolin na "Canton", wanda ake kallo a matsayin magwajin tasirin hada hadar cinikayyar waje ta kasar Sin. (Saminu)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China