Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An gudanar da taron muranr cika shekaru 75 da sanya hannu kan yarjejeniyar kafa MDD
2020-06-25 15:12:18        cri

Jiya Laraba ne aka kira taron wani dandalin murnar cika shekaru 75 da sanya hannu kan yarjejeniyar kafa MDD. Taron da ya gudana ta kafar bidiyo a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, ya zayyana muhimmancin kasancewar bangarori daban-daban, a daidai gabar da ake fama da COVID-19.

Masana da wakilan kungiyoyin kasa da kasa, sun hallara da kafar bidiyo, inda suka yi musayar ra'ayoyi kan karfafa alakar bangarori da dama, ta yadda za a cimma nasarar manufofin ci gaba mai dorewa tare.

Bugu da kari mahalarta dandalin, sun tabo batutuwa da dama, kamar bunkasa tsare-tsare karkashin jagorancin MDD da tunkarar kalubalen dake tattare da tafiyar da harkokin duniya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China