![]() |
|
2020-06-06 16:37:04 cri |
Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya nemi kasashen duniya, su kara taimakawa yankin Sahel yaki da ta'addanci da shawo kan tushen rashin kwanciyar hankali da ci gaba da kokarin warware matsalar siyasa a yankin.
Zhang Jun, ya ce har kullum, kasar Sin na mara baya ga ra'ayin warware matsalolin Afrika ta hanyoyin da suka dace da nahiyar, sannan tana fatan kasashen duniya za su ci gaba da martaba muradun al'ummun yankin Sahel da cikakken 'yancin kasashen yankin da kuma goyon bayan muhimmiyar rawar da hukumomi a yankin, kamar Tarayya Afrika, ke takawa.
Ya kara da kira da a yi kokarin magance kalubalen da ta'addanci da laifuffukan da ake aikatawa ke haifarwa a yankin.
Ya ce rundunar kawance ta kasashen yankin 5, ta taka muhimmiyar rawa, kuma Sin na goyon bayan shirin wanzar da zaman lafiya na MDD dake Mali, wajen taimakawa rundunar kawance, da kuma goyon bayan ra'ayin gyara ayyukan shirin na wanzar da zaman lafiya da samar da taimakon kudi da ake bukata dangane da hakan. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China