Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta bukaci kasashe mambobin MDD da su biya kudaden karo-karo da ya dace su biya
2019-10-11 19:13:15        cri

Kasar Sin ta yi kira ga kasashe mambobin MDD, da su biya kudaden karo-karo na majalisar da aka ware musu, bisa la'akari da yadda MDD ke fama da gibin kudi.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, shi ne ya bayyana hakan Jumma'ar nan, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa. Ya ce a matsayinta na kasa ta biyu mafi ba da gudummawa ga MDD, kasar Sin ta biya dukkan kudaden da ya kamata ta biya a shekara a matsayinta na mambar majalisar.

Ya ce, biyan irin wadannan kudade a kan lokaci, ya zama wajibi, domin ta haka ne za a tabbatar da tafiyar da ayyukan MDDr.

Geng ya ce, a matsayinta na kasar da ke ba da gudummawa mafi yawa, har yanzu ana bin Amurka bashin sama da dala biliyan 1.05 na kudaden karo-karon da ba ta biya ba, kimanin kaso 76 cikin 100 na dukkan kudaden da ba a biya ba. Yana mai cewa, ya kamata kasashe mambobin majalisar dake biyan kudaden karo-karon, su ba da gudummawa don magance matsalar kudaden da MDDr ke fama da ita.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China