Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na fatan kwamitin sulhun MDD zai dauki matakin daidaita batun zirin Koriya
2019-12-30 19:31:30        cri

A yau Litinin a nan birnin Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana cewa, kasar Sin tana sa ran cewa, kwamitin sulhun MDD, zai sauke nauyin dake wuyansa na tabbatar da kwanciyar hankali a zirin Koriya ta hanyar gudanar da tattaunawa.

Rahotannin sun bayyana cewa, kwamitin sulhun zai kira kwarya-kwaryar taro a yau, domin gudanar da tattaunawa karo na biyu, kan shawarar da kasashen Sin da Rasha suka gabatar, game da kawar da takunkumin da aka sakawa Koriya ta Arewa. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China