Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta kara ragewa masu son kafa kamfanoni dawainiya
2020-06-24 21:10:39        cri

Kasar Sin ta bullo da wasu sabbin matakai na kara rage lokacin da masu neman kafa kamfanoni ke bukata, da daidaita kudade da kungiyoyin kasuwanci ke karba, a wani mataki na rage musu dawainiya da kara musu karfi.

An dauki wannan mataki ne, yayin taron majalisar gudanarwar kasar da firaministan kasar ta Sin Li Keqiang ya jagoranta Larabar nan. Manufar daukar wannan mataki, ita ce rage lokaci da ake bukata wajen kafa kamfani, daga kwanaki biyar na ranakun aiki a halin yanzu, zuwa kwanaki 4 na kwanakin aiki ko kasa da haka.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China