![]() |
|
2020-06-23 20:11:22 cri |
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijiang, ya bayyana kudirin kasarsa na yin aiki tare da al'ummomin kasa da kasa, a wani mataki na ganin an aiwatar tsarin kasancewar bangarori daban-daban, da cimma manufar raya da kare hakkin dan-Adam, da inganta rayuwar al'ummomin kasashen duniya.
Ya ce, jiya ne, hukumar kare hakkin dan-Adam ta MDD ta sake amincewa da wani kudiri kan "bunkasa alakar cin moriyar juna a fannin kare hakkin dan-Adam", kudirin da kasar Sin ta gabatar, don mayar da martani kan tambayoyin da aka gabatar kan wannan batu.(Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China