Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Cibiyar kula da tsoffi ta Guli dake lardin Jiangsu na kasar Sin
2020-06-24 19:40:04        cri

A cikin cibiyar kula da tsoffi ta Guli mai fadin muraba'in mita sama da dubu 4 dake birnin Nanjing, fadar mulkin lardin Jiangsu na kasar Sin, a kan ji wakar da tsoffin dake zama a ciki suka rera kamar haka: "Akwai labarai masu yawa a karamin gari, ana rayuwa cikin dadi, idan ka zo nan, za ku samu sakamako masu kyau."

Fang Chuanfu, mai shekaru 78 da haihuwa ya shafe shekaru 7 yana rayuwa a cibiyar, daga fuskarsa mai cike da farin ciki, ana iya fahimtar cewa, yana jin dadi ko wace rana. Kaka Fang ya zo cibiyar kula da tsoffi ta Guli ne daga garin Guli na yankin Jiangning na birnin Nanjing, shi manomi ne, ya kuma rabu da matarsa.

Kaka Fang ya samu iznin zama a cibiyar ce saboda ba shi da yara, ba shi da karfin da zai yi aiki, sannan ba shi da kudin shiga, don haka tun daga shekarar 2013, ya fara zama a cibiyar Guli.

Lokacin da aka fara kafa cibiyar, dakunan da tsoffin ke zama ba su da inganci, ana kuma baiwa tsoffi abinci sau uku a ko wace rana, daga baya aka ci gaba da inganta cibiyar, kaka Fang ya kara jin dadin zamansa, yanzu haka ana ba shi kudin Sin yuan dari 5 a ko wane wata.

 

Yanzu ko wace rana tsoffin dake rayuwa a cikin cibiyar suna kallon fina-finai ko yin zane-zane ko wasan dara da kati, suna jin dadi matuka.

 

A lardin Jiangsu, adadin tsoffi ya kai miliyan 18 da dubu 340, adadin da ya kai kaso 23 bisa dari na daukacin mazauna lardin, kawo yanzu ana gyara cibiyoyin kula da tsoffi da yawansu ya kai 900 dake kauyukan fadin lardin, kuma za a kammala aikin cikin shekaru uku masu zuwa.

Kana gaba daya adadin cibiyoyin kula da tsoffi da aka gina a unguwanin fadin lardin Jiangsu ya kai dubu 18 da dari biyu, haka kuma, ana gina cibiyoyin kula da tsoffi da rana a unguwannin lardin da yawansu ya kai 589, ban da haka ana samar da hidimar kulawa a cikin gidajen tsoffi sama da miliyan 2 da dubu 290.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China