Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta zargi Indiya da karya yarjejeniyar da sassan biyu suka cimma
2020-06-24 20:07:52        cri

Ma'aikatar tsaron kasar Sin ta bayyana cewa, arangamar baya-bayan da ta auku tsakanin sojojin kasashen biyu a kan iyaka, ta faru ne sakamakon karya yarjejeniyar da sassan biyu suka cimma da Indiyan ta yi, ta kuma takali fada.

Mai magana da yawun ma'aikatar Wu Qian ne ya bayyana haka Larabar nan, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa wata-wata a birnin Beijing, yana mai kira ga sassan biyu da su kara azama wajen tabbatar da zaman lafiya a kan iyakar kasashen biyu.

Jami'ai daga ma'aikatar tsaron kasashen biyu, sun amince su dauki matakan da suka dace, don rage zaman tankiya a kwarin Galman mallakar kasar Sin, yayin ganawar da aka shirya gudanarwa a ranar 6 ga watan Yuni, amma sojojin kasar Indiya suka keta yarjejeniyar da aka cimma.

Wu ya bayyana cewa, ya shaidawa bangaren Indiya, da ya hukunta wadanda ke da hannu wajen aikata wannan danyen aiki, kana ya ladabtar da sojojin dake kan iyaka, don tabbatar da cewa, irin haka ba zai sake faruwa ba a nan gaba.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China