Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministan harkokin wajen Sin ya bukaci a cigaba da kyautata tattaunawa tsakanin Sin da Indiya don warware rikicin kan iyakoki
2020-06-18 13:02:44        cri
Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya bada shawarar karfafa tattaunawa tsakanin Sin da Indiya da yin hadin gwiwa game da yadda za'a daidaita batutuwan da suka shafi rikicin kan iyakokin kasashen, kana da yin aiki tare don tabbatar da samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankunan kan iyakokin kasashen biyu.

A tattaunawar da ya yi ta wayar tarho da ministan harkokin cikin gidan Indiya, S. Jaishankar, Wang ya ce, rundunar sojojin tsaron Indiya dake kan iyakokin kasashen a daren Litinin sun karya yarjejeniyar da aka cimma a babban taron tattauwa tsakanin hukumomin sojojin bangarorin biyu. A halin da ake ciki yanzu a yankin kwarin Galwan al'amura sun daidaita, haka zalika, sojojin kasar Indiya sun ketare ainihin kan iyakar kasar Sin da gangan da nufin yin tsokana, har ma sun kai hari kan jami'an kasar Sin kuma sojojin Sin da suka je yankin ne domin cimma daidaito, matakin da a zahiri ya haifar da rikici gami da hasarar rayuka.

Wang ya ce, mummunan yunkurin sojojin Indiya ya yi matukar saba yarjejeniyar da kasashen biyu suka cimma game da batun kan iyakokin kasashen da muhimman dokokin da suka shafi dangantakar kasa da kasa, sai dai ya bayyana cewa, kasar Sin tana adawa da yunkurin da bangaren Indiya ke nunawa.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China