Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Saudiyya ta haramtawa wadanda suka haura shekaru 65 aikin hajji bana
2020-06-24 14:20:33        cri
Kasar Saudiyya ta sanar da sharudan aikin hajjin bana a jiya Talata, inda ta ce maniyatta dake kasa da shekaru 65 ne kadai za a bari su yi aikin hajjin.

Ministan lafiya na kasar Tawfiq Al-Rabiah, ya shaidawa wani taron manema labarai cewa, ya kamata wadanda za su yi aikin hajjin su kasance kasa da shekaru 65, sannan ba su da wata rashin lafiya mai tsanani. Ya kara da cewa, sai kuma sun yi gwajin cutar COVID-19, kana bayan kammala aikin hajjin, za su killace kansu a gida.

Saudiyya ta sanar a ranar Litinin cewa, bisa la'akari da yaduwar cutar COVID-19 a duniya, kayaddadun mutane dake zaune a kasar ne kadai za a ba damar aikin hajjin a bana.

Baya ga haka, Ministan kula da aikin hajji da umarah na kasar, Mohammad bin Saleh Benten, ya yi bayanin cewa, masarautar Saudiyyar ta yanke shawarar ne domin kare lafiyar mahajjata. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China