Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Saudiyya ta ce dukkan maniyyata daga kasashen waje sun riga sun isa kasar
2019-08-08 10:23:34        cri

Kamfanin dillancin labarai na Saudi Press ya ruwaito gwamnatin Saudiyya ta sanar a jiya Laraba cewa dukkan maniyyatan hajjin bana daga kasashen waje sun riga sun isa kasar.

Darakta janar na hukumar kula da fasfo na Saudi, Sulaiman Al Yahya, ya fadawa taron manema labarai a Jeddah cewa ya zuwa yammacin ranar Laraba adadin maniyyatan da suka riga suka isa kasar ya kai miliyan 1.8.

Ya ce, kimanin maniyyata miliyan 1.7 sun isa kasar ne ta jiragen sama, yayin da maniyyata 95,634 suka isa Saudiyya ta kasa, sai kuma 17,250 da suka isa kasar ta ruwa, ya ce a wannan karo an yi amfani da wasu kwararrun jami'ai da kuma fasahohin zamani wajen bibiyar yadda harkokin alhazai ke gudana. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China