Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tawagar likitocin yaki da cutar COVID-19 ta Sin ta isa Saudiyya
2020-04-16 11:03:29        cri

A jiya da yamma, tawagar likitocin yaki da cutar COVID-19 da gwamnatin kasar Sin ta tura, ta isa birnin Riyadh, babban birnin kasar Saudiyya.

An ce, hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin ce ta kafa wannan tawaga, kuma masanan dake cikin ta sun kware a fannonin bincike a dakin gwaji, da yaki da cututtuka masu yaduwa, da cututtukan numfashi, da ba da jinya, da likitancin gargajiya na Sin da sauransu.

Tawagar masanan za ta more fasahohin kasar Sin, na yaki da cutar COVID-19 tare da kasar Saudiyya, ta hanyoyin yin ziyara, da bincike, da mu'amala bisa shirin da bangarorin biyu suka tsara, da kuma horaswa kan kandagarkin cutar, da ba da jinya ga masu dauke da ita. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China