Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Saudiyya ya yanke hukuncin kisa kan mutane 5 dake da alaka da kisan Jamal Khashoggi
2019-12-24 10:55:26        cri

Babbar hukumar gabatar da kararraki ta Saudiyya, ta ba da labari a jiya Litinin cewa, an yanke hukuncin kisa kan mutane 5, dake da alaka da kisan dan jaridar nan Jamal Khashoggi.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta bayar a wannan rana, an ce, kotun bincike manyan laifufuka ta birnin Riyadh ce ta yanke hukuncin kisan mutanen su 5, dake da hannu a hallaka Jamal Khashoggi, baya ga wasu mutane 3 kuma da aka yankewa hukuncin daurin shekaru 24, yayin da wasu 3 aka gano cewa ba su aikata laifi ba.

Wakilan iyalan Jamal Khashoggi, da wakilan ofishin jakadancin Turkiya dake Saudiyya sun saurari sakamakon hukuncin a kotu.

Jamal Khashoggi dan jarida ne dake gabatar da bayanan da ya rubuta ga kafofin yada labarai da dama, ciki hadda Washington Post. A ranar 2 ga watan Oktoban bara ne kuma, ya shiga ofishin jakadancin Saudiyya dake Turkiya, amma bai fito ba. Ranar 20 ga watan, hukumar gabatar da kararraki ta sanar da rasuwarsa. Kuma a ranar 25 ga watan Oktoban bara, babban mai gabatar da kara a kotu ya ce, an hallaka Jamal Khashoggi.

A ranar 15 ga watan Nuwambar bara, aka sanar da gabatar da kara kan mutane 11, da aka tuhuma da hannu a cikin laifin hallaka dan jaridar. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China