Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An fara gwajin sabon jirgin kasa mai tafiya da karfin magadanisu a Sin
2020-06-22 19:52:26        cri

Hedkwatar kamfanin CRRC Qiangdao Sifang, kamfanin da ya kera jirgin kasa mai tafiya da karfin maganadisu da ake kira Maglev, ya ce, an fara gwajin jirgin mai gudun kilomita 600 cikin sa'a guda a jiya Lahadi.

Jirgin mai taragu daya, zai duba da ma amfani da muhimman fasahohin kere-kere da tsare-tsare na maganadisu da zai rika amfani da su wajen tafiya tare da fito da wani muhiimin tushen aikin injiniya da za gwada a nan gaba.

A cewar kamfanin, yayin gwaji na farko da aka gudanar a jiya Lahadi kan layin dogo na jirgin, an yi nazarin sama da sassan jirgin 200, da suka hada da sakamakon aikin, da kananan kwane kwane da gangara.

Shugaban tawagar bincike da kera jirgin, Ding Sansan kana mataimakin babban injiniya na kamfanin CRRC Qingdao Sifang, ya bayyana cewa, binciken farko da aka gudanar ya nuna jirgin ba shi da wata matsala, kana dukkan muhimman alkaluma sun nuna cewa, an cimma sakamako da burin da aka sanya a gaba.

Kamfanin ya ce, aikin bincike da kera irin wadannan jirage na gwaji guda biyar na tafiya kamar yadda aka tsara. Ana kuma sa ran kammala su a shekarar 2020 da muke ciki.

Su dai irin wadannan jirage masu tafiya da karfin maganadisu, ba su da kara sosai, kamar jiragen kasa. Haka kuma, da'irar da suke tafiya rabin da na jirgin karkashin kasa ne, abin da ke ba su damar ratsa gine-gine yayin da ake tsara su. A watan Mayun wannan shekarar ce kamfanin CRRC ya kera wannan jirgin.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China