Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: Amurka na yawan ruwa wutar rikici a yankin tekun kudancin Sin
2020-06-03 20:17:24        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Zhao Lijian, ya ce Amurka ba ta cikin kasashe masu ruwa da tsaki, a takaddamar yankin tekun kudancin kasar Sin, amma duk da haka, tana yawan haifar da rashin jituwa a yankin.

Kaza lika Amurka na yawan gudanar da ayyukan soji na tsokanar fada a yankin, lamarin da a cewar Zhao, ba zai haifar da yanayin zaman lafiya da daidaito a yankin ba.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen na Sin, ya yi wannan tsokaci ne, bayan da sakataren wajen Amurka Mike Pompeo ya wallafa wani sako a shafin sa na Twita a jiya Talata. A cikin sakon na sa, Mr. Pompeo ya ce kasar sa, ta aikawa babban magatakardar MDD wata wasika, mai kunshe da nuna rashin yarda da matakin Sin, na karya ka'idojin martaba mulkin kai na kasashen dake yankin na tekun kudancin Sin. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China