Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Idan kana son danka, ya kamata ka yi masa tarbiyya yadda ya kamata
2020-06-20 21:37:07        cri

Marigayi Xi Zhongxun shi ne mahaifin shugaban kasar Sin Xi Jinping, wanda gwarzon dan juyin juya hali ne a kasar. Marigayi Xi Zhongxun ya kasance mahaifi da ke kaunar dansa, sai dai a waje guda, yana mai da hanhali a kan ba da misali ga dansa don koyar da shi, don haka, ya haifar da babban tasiri ga Mr. Xi Jinping.

A wata wasikar da Mr. Xi Jinping ya aikawa mahaifinsa don taya shi murnar ranar haihuwarsa, ya ce, "Akwai kyawawan halaye da dabi'u da dama da nake fatan karowa daga gare ka."

Mr. Xi Jinping yana martaba mahaifinsa sosai, ya kuma bayyana shi a matsayin "sa dake da hazakar aiki a gonar al'ummar kasar Sin", don haka, ya yi alkawarin "yin iyakacin kokarina don bauta wa al'ummar kasar Sin".

Marigayi Xi Zhongxun ya taba bayyana wa malam Xi Jinping cewa, "duk mukamin da ka hau, kada ka manta da bauta wa al'umma, ka dinga yin mu'amala da su."

Har kullum, al'ummar kasar Sin na cikin zuciyar marigayi Xi Zhongxun, yana kuma mu'amala da su. Don haka ma, shugaba Xi Jinping shi ma ya sanya jama'a a cikin zuciyarsa, kuma biyan bukatun al'umma ta fannin jin dadin zaman rayuwarsu shi ne aikin da ya sanya a gabansa.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China