Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bangaren ba da hidima na kasar Sin ya fara farfadowa a watan Mayu
2020-06-17 10:25:58        cri

Bangaren ba da hidima na kasar Sin, wanda annobar COVID-19 ta yi wa mummunan tasiri, na farfadowa sannu a hankali, yayin da kasar ke kokarin daidaita ayyukan yaki da cutar da na bunkasa tattalin arziki da zaman takewa.

A cewar hukumar kididdiga ta kasar, bangaren ya samu karuwar kaso 1 bisa dari a watan Mayu, wanda ya zama tagomashi na farko da ya samu a bana, bayan ya fuskanci koma baya da kaso 4.5 bisa dari a watan Afrilu.

Bangaren sadarwa da samar da manhaja da fasahar sadarwa, ya karu da kaso 12.9 bisa dari a watan da ya gabata, yayin da bangaren hada-hadar kudi ya karu da kaso 5.2 bisa dari, inda na samar da gidaje kuma ya karu da kaso 7.1 bisa dari. Baya ga haka, bangarorin dillancin da sayar da kayayyaki da na samar da abinci da na ba da haya da kasuwanci, su ma duk sun samu tagomashi a watan Mayu.

Kakakin hukumar Fu Linghui, ya ce ana sa ran kara samun farfadowa bangaren bisa la'akari da ci gaba da dawowar harkoki da zaman rayuwa kamar yadda suke a baya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China