Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Libya ta soki furucin kasar Masar, inda ta bayyana shi a matsayin takalar yaki
2020-06-22 13:43:06        cri
Gwamnatin Libya dake samun goyon bayan MDD, ta ce ta dauki furuci na baya-bayan nan da shugaban Masar Abdel-Fattah al-Sisi ya yi, a matsayin takalar yaki.

Cikin wata sanarwa da gwamnatin ta fitar, Libya ta jaddada cewa, ba za ta amince da tsoma baki cikin harkokinta na cikin gida ko keta cikakken 'yancinta ba, ta hanyar furuci, kamar yadda shugaban Masar ya yi, ko ta hanyar taimakawa aiwatar da juyin mulki ko taimakawa sojojin haya. Tana mai cewa, za ta dauki irin wannan yunkuri a matsayin takalar fada da ayyana yaki.

Sanarwar ta kara da cewa, gwamnatin hadin kan kasar ita ce halaltacciyar gwamnati dake wakiltar kasar Libya, kuma ita ce ke da hakkin tantance nau'o'in yarjeniyoyi da kawenta.

A ranar Asabar ne, shugaba al-Sisi na Masar, ya sanar da cewa sojojin kasarsa a shirye suke su shiga tsakani, su taimakawa Libya yaki da 'yan ta'adda da kungiyoyi masu dauke da makamai. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China