Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Libya mai samun goyon bayan MDD ta kaddamar da harin jiragen sama kan sansanin sojojin masu helkwata a gabashin kasar
2020-05-18 11:31:13        cri
Dakarun tsaron gwamnatin kasar Libya mai samun goyon bayan MDD ta sanar a ranar Lahadi cewa ta kaddamar da hare hare ta sama kan sansanin sojoji masu helkwata a gabashin kasar.

Mohamed Gonono, kakakin sojojin gwamnatin Libya da MDD ke goyon baya ya fada cikin wata sanarwa cewa, sojojin sama sun kaddamar da hare-hare kan sansanin sojojin sama a Watya da kewayensa dake kudu masu yammacin Libya.

Hare haren biyu sun lalata wasu wuraren ajiye kayan yaki a sansanin sojojin, wanda ke da tazarar kilomita 140 a kudu maso yammacin birnin Tripoli.

Haka zalika, dakarun sojojin masu sansani a gabashin kasar sun sanar da harbo jirgin Turkiyya marar matuka mallakin dakarun sojojin gwamnatin Libya dake samun goyon bayan MDD a birnin Ajaylat, mai nisan kilomita 80 a yammacin birnin Tripoli.

Sama da shekara guda ke nan, mayakan gwamnatin Libya da ke samun goyon bayan MDD ke cigaba da gwabza yaki da sojoji masu sansani a gabashin kasar dake neman kwace ikon birnin Tripoli, lamarin da yayi sanadiyyar kashe fararen hula masu yawa.

Duk da irin kiraye kirayen da kasa da kasa ke yi na neman tsakaita bude wuta, har yanzu ana cigaba da gwabza yakin kana ana hallaka fararen hula.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China