Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta jaddada bukatar amfani da matakan siyasa don warware rikicin Libya
2020-06-08 14:20:25        cri
Shirin wanzar da zaman lafiyar MDD a kasar Libya (UNSMIL), ya nanata bukatar amfani da matakan siyasa don warware rikicin kasar Libya, inda aka bukaci dukkan bangarorin da abin ya shafa da su amince da shiga tattaunawar sulhu ta hadin gwiwa da hukumar sojoji wadda MDD ta shirya.

Sanarwar UNSMIL ta ce, halin da aka shiga a kasar Libya sama da shekara guda ya kara tabbatar da cewa, daukar duk wasu matakan yaki a tsakanin al'ummomin kasar Libya ba zai haifar da da mai ido ba. Babu wani bangare a zahiri da zai yi ikirarin shi ne ke da nasara, idan ban da mummunar hasara da ake tafkawa ga kasar da mutanen kasar, inda mutanen kasar ke fuskantar matsanancin hali sakamakon tashin hankalin da aka shafe sama da shekaru tara ana fuskanta a kasar.

A cewar sanarwar, amfani da matakan siyasa wajen warware rikicin Libyan wanda ya ki ci ya ki cinyewa ita ce kadai hanya mai bullewa, shirin MDD a shirye yake ya jagoranci shirya tattaunawar sulhu wanda 'yan Libyan za su gudanar da zai kunshi dukkan bangarorin kasar ta Libya don warware takaddamar siyasar kasar.

UNSMIL ta tunatar da dukkan bangarorin kasar Libya game da muhimmancin mutunta dokar kasa, da dokokin kare hakkin dan adam na kasa da kasa, da dokokin da suka shafi aikin bada jin kan bil adama domin kare fararen hula da gine-ginen gwamnati, kamar asibitoci, makarantu, gidajen yari, musamman a halin da ake ciki game da yaki da annobar COVID-19.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China