Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta bukaci a tsakaita bude wuta na dindindin a Libya
2020-05-06 11:52:56        cri
Wakilin kasar Sin ya bukaci a tsakaita bude wuta na dindindin a kasar Libya, musamman bisa ga yanayin da ake ciki na yaki da annobar COVID-19.

Yao Shaojun, mai rikon mukamin mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD ya ce kamata yayi dukkan bangarorin dake yaki da juna a Libya su sanya bukatar kasa sama da komai kuma su baiwa rayuwar mutane muhimmanci fiye da komai kana su yi kokarin tabbatar da tsakaita bude wuta mai dorewa ba tare da bata lokaci ba. Bisa la'akari da halin da ake ciki a yanzu, mutanen kasar Libya sun cancanci samun yanayin zaman lafiya a kasar don tabbatar da yaki da annobar COVID-19 da ake fama da ita a duk duniya.

Yao, ya ce kasar Sin tana taimakawa kasar Libya kuma tana goyon bayan amfani da matakan siyasa don warware rikicin kasar, kuma tana karfafawa MDD gwiwa da kungiyoyin shiyya kamar kungiyar tarayyar Afrika da gamayyar kungiyar kasashen larabawa da su cigaba da aikin shiga tsakani domin samar da fahimtar juna.

Ya ce a ko da yaushe kasar Sin ta yi amanna cewa tilas ne a warware batun takaddamar kasar Libya ta hanyar matakan siaysa. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China