Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta bayyana damuwa kan mummunan harin da aka kai kan wani sansanin soja a Mali
2019-11-05 09:32:07        cri

Mataimakin kakakin babban sakataren MDD Farhan Haq, ya bayyana cewa, MDD ta kadu matuka game da wani hari da aka kai kan wani sansanin soja a Indelimane dake yankin Menaka a kasar Mali, inda aka halaka gomman sojoji.

Haq ya shaidawa taron manema labarai cewa, bayanan da suka shigo hannu na nuna cewa, gomman sojoji ne suka rasa rayukansu, uku sun jikkata, kana har yanzu ba a ji duriyar wasu guda biyu ba. Baya ga wani farar hula da aka kashe, guda kuma ya ji rauni.

Ya bayyana cewa, tawagar MDD dake aikin tabbatar da zaman lafiya a Mali (MINUSMA) ta tura dakarun kai daukin gaggawa don taimakawa 'yan kasar tabbatar da tsaro a yankin da lamarin ya faru, da gudanar da bincike da ma aikin ceto.

Ministan sadarwa na kasar Mali, Yaya Sangare, ya bayyana cewa, mutane 53 aka kashe a harin da aka kai a nisan kimanin kilomita 70 yamma da Menaka. Sojoji sun bayyana harin na Jumma'ar da ta gabata a matsayin mummunan harin ta'addanci.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China