Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dokar Amurka kan yankin Xinjiang na Sin ta saba dokar kasa da kasa, in ji tsohon jakadan Masar
2020-06-21 17:11:18        cri

Kudirin dokar da Amurka ta sanyawa hannu kwanan nan kan jihar Xinjiang mai cin gashin kai ta kasar Sin, ya saba yarjejeniyar dokar MDD, kana ya ci karo da hakkin kasar Sin na iko da yankunanta, wani jami'in kasar Masar shi ne ya bayyana hakan a zantawar da ya yi kwanan nan da kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

"Wannan kudurin dokar ya saba ka'ida kuma haramtacce ne saboda majalisar wakilan Amurka ce ta zartar da dokar ga wata kasa ta daban. Ko gwamnatin Amurka ko kuma majalisar wakilan kasar ba su da ikon zartar da kudirin dokar da za'a aiwatar a wasu kasashen duniya," a cewar Mohamed Noman Galal, mamban majalisar harkokin kasashen waje na kasar Masar.

Kudirin, mai taken "Dokar hakkin dan adam ta Uygur ta 2020," ta fuskanci kakkausar suka daga gwamnatin kasar Sin da al'ummar Sinawa.

Galal, tsohon jakadan Masar a kasar Sin, ya ce ya sha kaiwa ziyara zuwa jihar Xinjiang a lokuta da dama, ziyarar da ya kai ta baya bayan nan ita ce a shekarar 2014, inda yanayin tsabtar tituna da kayan marmari masu dadin sha da yanayin zaman lafiyar mazauna Xinjiang sun yi matukar burge shi.

Ya ce, "Na ziyarci masallatai masu yawa a Xinjiang kuma na ga mutanen yankin suna gudanar da ayyukan ibadunsu ciki 'yanci. Amma idan har wani daga cikinsu ya aikata wani abu da ya saba doka ko kuma ya aikata ta'addanci, tilas ne a hukunta shi kamar yadda ake hukunta kowane basine idan ya aikata ba daidai ba".

A cewarsa, kasar Sin tana da 'yancin tinkara da kuma dakile duk wasu nau'ikan ta'addanci ko kawo baraka, babu wata kasa a duniya da za ta laminta, har da ita kanta Amurkar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China