Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yankin Xinjiang yana ba da muhimmanci kan batun ilimi
2020-01-20 20:06:54        cri

Mai magana da yawun ofishin watsa labarai na gwamnatin al'ummar yankin Xinjiang na kabilar Uygur mai cin gashin kansa na kasar Sin Elijan Anayit, ya bayyana cewa, mahukuntan yankin suna dora muhimmanci kan batun ilimi.

Elijan ya bayyana cewa, yawan yaran da suka shiga makarantar reno a yankin, ya kai kaso 95.95 cikin 100 sai kaso 99.9 na yaran da suka kai shiga makaranta da aka sanya a makarantu. Yankin ya cimma nasarar tsarin nan na shekaru 9 na ilimi tilas kana yankuna 4 dake kudancin Xinjiang sun samar da shekaru 15 na ilimin kyauta ga dukkan yara dake makarantun reno zuwa babbar makarantar midil.

A game da matakan da yankin ya dauka don bunkasa yin magana da rubutu da daidaitaccen Sinanci, shugaban kula da harkokin hukumar ilimi na yankin Kashgar Enwer Ablimit, ya bayyana cewa, dokokin kasar Sin sun zayyana cewa, wajibi ne ko wane Basine ya koya ya kuma yi amfani da daidaitaccen Sinanci, yayin da jihar za ta samar musu da ka'idojin amfani da shi.

Ablimit ya bayyana cewa, tsarin koyon Sinanci na bai tsaya a kasar, ya saukaka sadarwa da hade al'ummomin dake karkaka cikin al'umma ta zamani. Ya kuma karyata rahotannin da kafofin watsa labaran Amurka ke watsawa, inda suke zargin cewa, kasar Sin tana kokarin kawar da yaren kabilar Uygur da Sinanci. Jami'in ya yabawa matakan da makarantun yankin suke dauka, inda dalibai da dama suka taimakawa iyayensu sanin abin da ke faruwa a duniya, ta hanyar kawar da matsalar yaren. Ya kara da cewa, yankin na Xinjiang ya kuma kare 'yancin daliban kananan kabilu na koyon harshensu, inda ake amfani da harsunan Uygur, Kirgiz da Mongol, Xibe wajen koyar da dalibai a makarantun firamare da na midil.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China