Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwararru sun yi Allah wadai da dokar Amurka kan yankin Xinjiang na Sin
2020-06-21 17:02:04        cri

Masanan kasa da kasa sun yi Allah wadai da kudirin doka mai taken "Dokar hakkin dan adam ta Uygur ta 2020" wanda Amurka ta sanyawa hannu, an bayyana rashin gamsuwa da dokar saboda yin shisshigi a harkokin cikin gidan kasar Sin.

A ra'ayin Andrei Manoilo, farfesa a fannin kimiyya siyasa a jami'ar Moscow, ya ce Amurka tana kallon kasar Sin a matsayin wata babbar abokiyar takara kuma ta jima tana yunkurin neman hanyar da za ta haifarwa kasar Sin koma baya.

Ya ce yayin da kasar Sin take ta kokarin yaki da ta'addanci da masu tsattsauran ra'ayi, kasar Amurka tana ta kokarin yiwa aikin yaki da ta'addancin da matakan kandagarkin da Sin ke dauka gurguwar fassara inda take nuna matakan na kasar Sin a matsayin take hakkin bil adama.

Shi ma Peter Kagwanja, shugaban cibiyar tsara manufofin Afrika na kasar Kenya, masanin na Afrika ya bayyana a lokacin zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, a ko da yaushe Amurka tana amfani da kalmar hakkin dan adam a matsayin wani makami wanda take kaddamar da hari kan abokan hamayyarta.

Sabanin ikirarin da Amurka ke yi, kasar Sin tana dora muhimmanci kan batun hada kan al'ummar kananan kabilu da bunkasa ci gaban al'adun kabilu daban daban, kuma matakan da kasar ke dauka game da batun yaki da ta'addanci da masu tsattsauran ra'ayi suna haifar da kyawawan sakamako.

Kasar dake bayyana kanta a matsayin mai rajin kare hakkin dan adam ta duniya, Amurkar ta rufe idonta kan muhimman batutuwan da suka shafi nuna wariyar launin fata da take hakkin bil adama dake faruwa a cikin kasarta, kamar abin da ya faru kwanan nan na kisan gilla kan ba'amurken nan bakar fata, lamarin da ya haifar da zazzafar zanga zanga a fadin duniya.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China