Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: Babu wani ma'aunin da zai dace da duk wani halin da ake ciki a duniya wajen kare hakkin dan Adam
2020-02-27 20:08:22        cri

A jiya Laraba ne Birtaniya, da wasu kasashe na daban, suka furta wasu kalamai na karya game da batun jihar Xinjiang, a gun taron koli karo na 43, na kwamitin kare hakkin Bil Adama na MDD da ya gudana a birnin Geneva.

Game da hakan, wakilin musamman na ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin mai kula da batun kare hakkin Bil Adama Liu Hua, ya yi jawabi a gun taron, inda ya bayyana matukar rashin jin dadinsa, tare da nanata cewa, wadannan kasashe sun yi biris da hakikanin halin da ake ciki, kuma sun tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin, game da ikon kasar na aiwatar da shari'a da doka, don haka ko kadan Sin ba za ta yarda da hakan ba.

Liu Hua ya nuna cewa, jihar Xinjiang ginshiki ne mai tushe ga kasar Sin. Tun shekaru 90 na karni na 20, an rika samun tasirin masu son kawo baraka tsakanin al'ummar Sinawa, da 'yan ta'adda, da kuma masu tsautsauran ra'ayin addini na kasashen ketare. Wadannan sassa sun rika ta da zaune tsaye a jihar Xinjiang, Wanda hakan ya haddasa asarar rayuwa da dukiyoyi da dama, kuma ya keta hakkin Bil Adama kwarai da gaske.

Jami'in ya ce gwamnatin kasar Sin na dauka wasu matakan da suka dace, don kawar da ta'addanci da tsautsauran ra'ayi, ciki hadda kafa cibiyoyin koyon fasahohin sana'o'i, wadanda suka ba da gudunmawa sosai ga kiyaye tsaron jihar, da ba da tabbaci ga kare hakkin jama'ar Xinjiang, wanda hakan ya sa, mazauna Xinjiang ke matukar maraba da wadannan matakai. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China